Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

An Yi Murnar Zagayowar Shekara Guda Da Boren Kin Jinin Al’bashir A Sudan 🇸🇩

A Sudan, dubun dubatar ‘yan kasar ne a sassan daban daban ke gangamin murnar cika shekara guda cif da soma boren da ya kai ga kifar da mulkin tsohon shugaban kasar Omar el-Bechir, wanda ya shafe shekaru talatin yana mulkin kasar.

Masu gangamin dake dauke da hotunan wadanda suka mutu a yayin zanga zangar data kai ga kifar da gwamnatin el-Bechir, na masu bukatar da a hukunta duk wadanda ke da hannu wajen kisan masu zanga zanga.

An kebe jiragen kasa guda biyu, wandanda sukayi jigilar jama’a zuwa yankin Atbara dake arewa maso gabashin kasar, inda nan ne aka fara zanga zangar kin jinin gwamnatin ta El-bashir a watan Disamba na shekara 2018 data gabata.

Za’a kwashe kwanakin na a yankin na Atbara har zuwa ranar 25 ga watan nan ana bikin murnar zagayowar lokacin soma boren wanda ya samo asali daga kara farashin bredi.

A wani rahoto data fitar hokumar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty Int. ta ce akalla mutane 177 ne aka kashe a wajen murkushe masu zanga zanga da gwamnatin ta Al-bashir.

A ranar 11 ga watan Afrilun da ya gabata ne sojoji suka kifar da gwamnatin ta Al-bashir.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu