Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

An Yi Taho Mu Gama Tsakanin Yan Sanda Da Masu Zanga -zanga a Kasar Labanon Mutum 14 Sun Jikkata


Rahotanni da ke fitowa daga birnin Berut na kasar labanon sun bayyana cewa jamai’an yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da harsashin roba wajen tarwatsa daruruwan masu zanga – zangar nuna kin jin gwamnati saboda kasa shawo kan Matsalar tattalin arziki da ke addabar kasar.

Kungiyar ba da agaji ta red Cross ta kasar ta labanon ta bayyyana cewa kimanin mutane 14 ne suka jikkata a lokacin taho mu gama din da aka yi, a tsakiyar birnin berut babban birnin kasar, inda guda 6 daga cikinsu suna kwance a Asibiti suna karbar magani.

Rahotanni sun tatabar da cewa an aike da karin jami’an tsaro a sauran sassan daban daban na kasar domin tunkarar masu zanga zangar, kuma zanga zangar ta barke ne tun bayan da tsohon fira minsitan kasar da ya yi murabus Sa’ad Hariri ya sanar da aiwatar da wani sabon tsarin karbar haraji a dai dai lokacin da alummar kasar ke cikin matsanancin halin tattalin arziki

Post a Comment

0 Comments

Close Menu