Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Ana Zaman Makoki Bayan Rasuwar Babban Hafsan Sojan Aljeriya

A Aljeriya, an fara zaman makoki na kwanaki uku, biyo bayan rasuwar babban hafsan sojin kasar, Janar Ahmed Gaid Salah, wanda ya rasu a cikin daren ranar Lahadi zuwa jiya Litini, sakamakon bugun zuciya.

Domin juyayin rishin ne, sabon shugaban kasar ta Aljeriya, Abdelmajid Tebboune ya kaddamar da zaman makoki na kwanaki uku a duk fadin kasar.

Tuni dai shugaban kasar ya nada Janar Said Chengriha mataimakin babban hafsan sojan kasar a matsayin sabon shugaban hafsan soja na wucin gadi.

Janar Gaid Salah wanda ya rasu yana da shekaru 79, ya kuma kasance a sahun gaba na hukumar mulkin sojan da ta jagorancin kasar har ya zuwa zaben sabon shugaban kasa na ranar 12 ga wannan wata na Disemba wanda Abdelmajid Tebboune ya lashe.

kuma ya kasance jigo a harkokin mulkin kasar tun daga shekara ta 1962, sannan ya taka muhimmiyar rawa wajen tilasta wa Shugaba Abdelaziz Bouteflika yin murabus a watan Aprilun da ya gabata a bisa matsin lambar masu zanga-zangar neman sauyi, ba tare da juyin mulki ba.

Saidai babbar ayar tambayar da ake azawa a yanzu, ita ce ko rasuwar tasa zata kawo karshen zanga zangar da aka jima anayi ta kyammar zaben shugaban kasar da masu boren ke dangantawa da haramtacce.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu