A jiya Laraba, 25 ga watan Disamba, mabiya addinin Kirista, sun gudanar da bikin kirsimiti, domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Isa, (AS).

Jagoran mabiya addinin na Krista, Paparoma Francis ya yi jawabi a cikin daren Talata da ya gabata.

A kasashen duniya da dama an tsauraren matakan tsaro domin baiwa amabiya addinin na krista damar gudanar da bukukuwansu.

Ranar Kirsimati dai rana ce da mabiya addinin kirista ke gudanar da bukukuwa da yin ibada da addu'o'i da kuma ziyarar juna domin nuna godiya ga mahalicci.

Tun kafin zuwan ranar kirsimeti dai, kirista kan mayar da hankali wajen kintsawa domin tunkarar wannan rana.

Lokacin kirsimeti dai, lokaci ne da malaman addini kan mika sako ga mabiya domin inganta kyawun zamantakewa da kwanciyar hankali.