Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Atisayen Soja Tsakanin Iran, Rasha Da China Sako Ne Babba Ga Amurka..A wata kasida da jaridar “Ra’ayul Yaum” ta yau Alhamis ta buga, ta bayyana atisayen hadin guiwa a tsakanin kasashen Iran, Rasha da China da cewa; masomin karshen ikon Amurka da yankin Tekun Pasha ne.

Iran ta sanar da cewa a ranar 27 ga watan nan na Disamba ne kasashen uku za su gudanar da rawar daji ta hadin guiwa akan doron ruwa tekun India, wadda ita ce irin ta ta farko a tsakanin kasashen.

Kasar Sin wacce take a matsayin mafi sayen man fetur a duniya,tana hankoron kare hanyoyin da take shigar da man fetur da take saye ne daga kasashen duniya zuwa cikin kasarta.

Masana sun bayyana cewa wannan atisayen zai kuma kawo karshen cin kare babu babbaka da rundunar sojan ruwan Amurka da take kasar Bahrain ke yi a cikin yankin tekun India da kuma gabar ruwan tekun pasha.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu