Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

(AU) Ta Koka Kan Matsanancin Tasirin Sauyin Yanayi A Afirka


Wata sanarwa da kungiyar tarayyar Afirka ta AU ta fitar a jiya Laraba, ta tabbatar da karuwar tasirin sauyin yanayi a kasashen dake nahiyar cikin shekaru kusan 20 da suka gabata.

Sanarwa ta ce hakan na yin mummunan tasiri ga zamantakewa da tattalin arzikin kasashen nahiyar.

AU ta ce duk da irin ci gaba da ake samu a fannin raya tattalin arziki da jin dadin jama'a a nahiyar, har yanzu Afirka na da rauni game da tunkarar matsalolin sauyin yanayi, tana kuma gamuwa da bala'o’I iri daban daban masu nasaba da sauyin yanayi.

Kaza lika wannan matsala na yin tarnaki ga burin cimma ajandar kasashenta nan da shekarar 2063, da ma kudurorin dake kunshe cikin shirin samar da ci gaba mai dorewa na kasa da kasa.

Sanarwar ta AU ta ce, kungiyar na jaddada muhimmancin aiwatar da yarjejeniyoyin kasa da kasa na dakile tasirin sauyin yanayi, ciki hada da yarjejeniyar Paris, da tsarin aiki na Sendai, da kudurorin wanzar da ci gaba.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu