Ayatullah Jawadi Amuli wanda daya ne daga cikin manyan malaman addinin musulunci a Iran, ya gana da ‘ya’yan malam Zakzaky jagoran harkar musulunci a Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky.

A yayin ganawar, Ayatullah Jawadi Amuli ya fadawa ‘ya’yan Sheikh Zakzaky cewa; Aikin da Sheikh Zakzaky ya ke yi a Nigeria mai girma ne, kuma Allah zai taimaka masa
Bugu da kari ya ce; Daga cikin ayyukan sadaukarwa da Sheikh Zakzaky ya yi saboda musulunci da akwai shahadar ‘ya’yansa shida, da kuma raunukan da ya samu a jikinsa da kuma tsare shi da aka yi.”

Babban malamin addinin musuluncin ya kuma ce; Da akwai samun sauki bayan kowane tsanani da wahala, kuma hakan alkawari ne na Allah.”

A karshen ganawar, Ayatullah Jawadi Amuli ya roki Allah madaukakin sarki akan samun saukin Sheikh Zakzaky da kuma sakinsa daga kurkuku.