Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Babban Zauren M D D Ya Bukaci Kasar Amurka Ta Janye Takunkumi Kan Jami’an Diplomasiyar Iran

Rahotani sun bayyana cewa a wani kuduri da babban zauren M D D ya fitar yayi kira ga kasar Amurka da ta janyen takunkumin da ta kakabawa jami’an Diplomsiyar kasar Iran, kudurin da kasar Cyprus ta gabatar a madadin kasahen Canada, Bulgeria, Costa Rica da ku kuma kasar Ivory Coast ya samu goyon baya, inda aka amince da shi ba tare da kada wata kuri’a ba.

Shi dai kudurin babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ba tilas ba ne amma yana da matsayin mai girma a bangaren siyasa.

Kudirin da bai fito fili karara ya ambaci sunan wata kasa ta musamman ba, sai dai jami’an diplomasiyya sun bayyana cewa an yi shi ne domin neman dauke takunkumin da Amurka ta kakaba wa jami’an diplomasiyan kasar Iran, da kuma hana (visa) shedar izini ga tawagar kasar Rasha wajen halartar taron babban zauren Majalisar da aka gudanar a watan satumbar da ya gabata.

Tun a lokacin bazara ne kasar Amurka ta kakaba takunkumin hana tafiye- tafiye ga wasu jami’an diplomasiyar kasar Iran ciki har da ministan harkokin wajen kasar a wata ziyara da ya kai Amruka, inda suka takaita da yankin da hedkwatar majalisar dinkin duniya take kawai a birnin New York.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu