Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Babbar kotu A Algeria Ta Tabbatar Da Abdulmajid Tabboune A Matsayin Zababben Shugaban Kasar


Rahotanni dake fitowa daga birnin Alges na kasar Algeria sun bayyana cewa babbar kotun koli ta tsarin mulkin kasar ta tabbatar da Abdumajid Taboune a matsayin sabon shugaban kasar da aka za’aba a wani wa’adin mulki na shekaru 5, duk da Zanga- zangar adawa da zaben da aka rika yi, da kuma kauracewa rumfunan zaben.

Tabounea ya lashe zaben ne da babbar rinjaye inda ya samu kashe 58% na dukkan kuri’un da aka kada. Babbar kotun ta bayyana cewa an gudanar da zaben cikin yanayi mai kyau sai dai bat ace komai game da zanga zangar da ake kwashe watanni ana yi a fadin kasar bat a nuna adawa da zaben.

Wannan dai shi ne ya kawo karshen mulkin tsohon shugaban kasar Albdulaziz Bouteflika bayan shekaru 20 da ya kwashe yana mulkar kasar dake da arzikin danyen man ferur. Sai dai masu Zanga- zanga sun yi watsi da nasarar da Taboune ya samu tun da ya taba zama Firai minista a tsohuwar gwamnatin da ta gabata.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu