Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Babu Shirin Tattaunawa Da Amurka A ziyarar shugaban Iran Zai Kai Kasar Japan 🇯🇵


Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Abbad Araqchi da yake ganawa da manema labarai a bayan taro kan kasuwanci tsakanin kasashen Iran da Japan da aka gudanar a jiya litinin anan birnin Tehran, ya yi karin haske game da yiwuwar ganawa tsakanin Amurka da shugaban kasar Iran Hassan Rouhani da zai kai ziyara kasar Japan anan gaba, inda ya nuna cewa babu wani shirin makamancin haka, domin ziyarce ta aiki, kuma zai kasance a kasar Japan ne kashe da saoi 24,kuma babbar manufar ziyarar Ita ce kara fadada dangantakar dake tsakanin kashen biyu da kuma tattaunawa game da batutunwan da suka shafi yankin dama duniya baki daya.

Har ila yau ya ci gaba da cewa shugaban Iran zai kai ziyara kasar Japan ne a ranar juma’an nan mai zuwa domin amsa gayyatar da Firai Ministan kasar Shinzo Abe ya yi masa, da kuma rama wa kura aniyarta na ziyara da ya kawo Tehran a watan Yuni shekara da muke ciki ta 2019.

Kasar Japan dai tana daga cikin manyan kasashen dake siyan man fetur din kasar Iran,kuma alakar kasashen biyu ta faro ne tun tsawon karnoni da suka gabata. Sai dai takunkumin da Amurka ta kakaba wa Iran na kawo cikas sosai huldar cinikayya dake tsakanin kashen biyu musamman ma a bangaren siyan man fertur

Post a Comment

0 Comments

Close Menu