Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Birtaniya na binciken yadda aka sako maharin gadar Landan An daure Usman Khan a shekarar 2012


Ma'aikatar Shari'a a Birtaniya ta kaddamar da wani binciken gaggawa domin gano yadda aka saki wanda ya kai harin ta'addanci a kan gadar birnin Landan, bayan an yanke masa hukuncin shekaru 16 a kurkuku a baya.

Maharin da aka bayyana sunansa da Usman Khan ya kashe mutum biyu, ya kuma jikkata wasu uku da wuka a kan gadar kafin 'yan sanda suka yi nasarar harbe shi.

Harin a yanzu ya tada hukumomin tsaron Burtaniya tsaye, makonni biyu kafin gudanar da babban zabe.Firai minista Boris Johnson da Sakatariyar Harkokin Cikin Gida Priti Patel
Rahotanni sun bayyana cewa an taba yankewa Usman Khan shekaru 16 a gidan kaso bayan da aka same shi da laifin ta'addanci a shekarar 2012, amma bai fi rabin wa'adin ba aka sake shi.


Shugaban jam'iyyar adawa ta Labour Jeremy Corbyn
Yanzu haka 'yan siyasa na kan tada jijiyoyin wuya da gwamnati kan yadda wannan baraka ta faru da kuma masu alhaki.

KNPRSCD 08
Kaduna press

Post a Comment

0 Comments

Close Menu