Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Yan Sahayuna Sun Kame Shugabanin Kungiyar Hamas A Gabar Kogin Jodan


Dakarun tsaron Sahayuna sun yi awan gaba da wasu shugabanin kungiyar gwagwarmayar Falastinawa wato a gabar tekun jodan.

Tashar talabijin din Al-Alam ta habarta cewaa wannan alhamis jami'an tsaron haramtaciyar kasar Isra'ila sun kai farmaki garin Al-khalil dake yankin gabar tekun jodan tare da wasu manyan shugabanin kungiyar gwagwarmayar Falastinawa Hamas biyar cikinsu kuwa harda manbobin Majalisar samar da dokokin Falastinu
Rahoton ya ce mafi yawa wadanda aka kame, sun taba zaman gidan kaso na haramtaciyar kasar Isra'ila.

A wani yunkuri na fadada mamayarta, a ko wata rana gwamnatin sahayuna na kai farmaki yankunan Falastinawa tare da kame wani adadi daga cikinsu.

A halin da ake ciki, kimanin falastinawa 5700 ke cikin gidajen haramtaciyar kasar Isra'ila 47 daga cikinsu Mata ne yayin da 250 kananen yara ne.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu