Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Daruruwan Yahudawan Sahayoniya Sun Kutsa Cikin Masallacin Kudus


A yau Talata ne ‘yan sahayoniya 229 su ka kutsa cikin masallacin kudus ta hanyar kofar “Babul-Magaribah” a karkashin cikakken tsaron ‘yan sanda.

Cibiyar da take kula da masallacin na Kudus ce ta tabbatar da kutsen ‘yan sahayoniyar da safiyar yau Talata, inda su ka rika yin ibadunsu na yahudanci a ciki, tare da bayyana hakan a mastayin tsokana.
A gefe daya, ‘Yan sandan HKI sun kame wasu samarin palasdinawa 10 a kusa da masalalcin na Kudus, da su ka hada da ‘yan mata.

Kutsen da yahudawan sahayoniya su ke yi cikin masallacin kudus ya zama ruwan dare, inda daga lokaci zuwa lokaci ‘yan sanda kan yi musu rakiya ciki.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu