Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Dubban Mutane Sun Yi Jerin gwanon Nuna Goyon Bayan Tsiga Shugaban Amurka


Adaidai lokacin da ake ta ja ni in ja ka game da batun tsige shugaban kasar Amurka Donald Trumph daga kan mukaminsa, kimanin mutane 200,000 ne suka gudanar da Zanga - zanaga a yankuna daban-daban na kasar Amruka domin nuna goyon bayansu ga tsige shugaban na Amurka da suka kira shi da makaryaci.

Duk da ruwan sama da aka yi da kuma tsananin sanyi da ake fama da shi amma bai hana dubban mutane fitowa kan tituna a biranen New York da sauran jihohin kasar ba, inda suka rika rera taken kira ga Trumph da ya fice daga fadar White House, suna masu sanar da cewa mun gaji haka, ba zamu sake yin hakuri har shekara mai zuwa ba, ku tsige shi yanzu.

A wata wasika da ya aikewa shugabar jamiyyar Democrat a majalisar wakilai Nancy Plosi Donald Trumph shugaban Amurka ya fadi cewa ba a yi masa adalci ba game da yunkurin tsige shi da ake son yi alhali shi bai aikata laifin komai ba, kana ya yi zargin cewa ana son yi masa juyin mulki ne kawai da karfin tsiya.

Ana zargin Trump ne da yin amfani da mukaminsa ba bisa Ka’ida ba, da kuma bada taimakon soji na dala miliyan 391 ga shugaban kasar Ukrain domin.

gudanar da bincike kan abokin hammayar siyasarsa Joe Biden tsoho mataimakin shugaban kasar, sai dai ya bayyana
zargin a matsayin bita da kulli ne kawai

Post a Comment

0 Comments

Close Menu