Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Dubban Mutanen Kasar Gambia Sun Yi Zanga-zangar Kira Ga Shugaba Adama Barrow Da Ya Yi Murabus


Mutanen kasar ta Gambia sun bazama akan babban birnin kasar Banjul suna masu yin kira ga shugaba Adama Barrow da ya sauka, tare da bayyana cewa; shekaru uku da ya yi akan mulki ya gundire su.

A lokacin da Adama Barrowa ya hau kan karagar mulkin kasar a farkon shekarar 2017, mafi yawancin al’ummar kasar suna daukarsa a matsayin mai ceto, bayan mulkin shugaba Yahya Jammeh na tsawon shekaru 22.

Barrow ya yi wa al’ummar kasar alkawalin kyautata rayuwarsu sannan kuma da tabbatar da tsarin mulkin demokradiyya, sannan kuma ya kafa kwamitin sulhulta al’ummar kasar.

Bugu da kari Adama Barrow ya yi wa al’ummar kasar tasa alkawalin cewa zai yi mulkin shekaru uku ne kadai, sai dai tuni ya take wancan alkawalin nasa,inda a yanzu ya ke kan wa’adin mulki na shekaru biyar da zai kare a 2021.

Da dama daga cikin mutanen kasar sun dawo rakiyar shugaba Barrow saboda sauya ra’ayi da ya yi akan tsawon lokacin da zai yi mulki.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu