Kasar Ethiopia ta sanar da cewa ta sami gagarumin ci gaba cikin ginin katafariyar madatsar ruwan nan na GERD wanda wani bangare ne na tsarin gina madatsar nan na Nilu duk kuwa cewa har yanzu ana ci gaba da tattaunawa kan madatsar ruwan.

Kasar Ethiopian ta sanar da hakan ne bayan wata ziyara da wata tawaga ta ‘yan majalisar kasar suka kai wajen da ake gina wannan madatsar ruwar ta dala biliyan 4 wacce aka fara gina ta a shekarar 2011 a kokarin kasar Ethiopian na zama kasar Afirkan da ta fi sauran kasashen nahiyar samar da makamashin wutar lantarki.
Ya zuwa yanzu dai an kammala kusan kashi 70% na aikin gida madatsar wacce ake sa ran za a gama da kuma bude ta a shekara ta 2023.

Gina madatsar dai ta janyo kace-kace tsakanin kasar Ethiopian da kasashen Masar da Sudan wadanda suke ganin gina madatsar ruwan zai cutar da kasashen su a bangaren samar da ruwa musamman kasar Masar wacce take ganin gina madatsar ta GERD za ta kara sanya kogin Nilu cikin matsalar kwaranyewar ruwa da yake fuskanta.