Kwamitin kungiyar tarayyar turai ya sanar a jiya Litini da janye kamfanonin jiragen saman kasar Gabon daga cikin jerin kamfanonin da aka haramtawa keta hazon kasashen turan.

Matakin dai ya shafi kamfanoni hudu na kasar ta gabon, da suka hada da (Nationale Régionale Transport, Solenta Aviation Gabon, Tropical Air Gabon da Afrijet Business Service), a cewar kakakin kungiyar ta (EU).

Tun a cikin shekara 2008 ne kungiyar ta (EU), ta sanya kamfanonin jiragen saman na kasar Gabon a cikin jerin kamfanonin da aka haramta wa shiga turai.

Saidai a sanarwar da ta fitar jiya, kungiyar ta (EU), ta ce ta janye haramcin saboda ci gaban da aka samu a kasar ta Gabon a fannin harkokin sufirin jiragen sama kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada.

A cikin sanarwar data fitar, kwamishiniyar kungiyar ta (EU), kan harkokin sufiri, ta ce ta yaba da kokarin hukumomin kasar ta Gabon.