A wani lokaci yau, Litini ne ake sa ran shugaban kasar Faransa Emanuel Macron, zai gana da takwarorins na kasashen Rasha da kuma Ukraine a fadar Elysee.

Wannan dai wani yunkuri ne na farfado da zaman lafiya tsakanin kasashen gubu dake zaman doya da man ja.

Taron na samun halartar shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da kuma na Ukraine, Volodymyr Zelenskiy, da kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a wani bangare.

Taron dai zai kasance irinsa na farko tun bayan shekara 2016, inda kuma ake sa ran shugaba Putin da Zelenskiy zasu gana a karon farko.