Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Faransa Ta Kai Harin Farko Da Jirgi Mara Matuki A Mali


Ma'aikatar Tsaron Faransa ta ce ta kai wani hari irinsa na farko da jirgi mara matuki, samfarin Reaper, da ya hallaka masu ikirari da sunan jihadi da dama a tsakiyar Mali a karshen makon da ya gabata.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar tsaron Faransar ta fitar jiya Litinin ta ce harin na jirgi mara matuki an kai shi ne a ranar Asabar a lokacin da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron yake ziyara a makwabciyar kasar Ivory Coast, inda Faransa ta ke da sansanin sojanta.

Aikewa da jiragen marasa matuka yana zuwa ne wata daya bayan da jiragen Faransa masu saukar ungulu guda biyu suka yi karo a Mali, da ya kashe sojoji 13.
A ranar Alhamis data gabata ne Faransa ta sanar da gwada harin farko da irin wandanan makamman da ake sarafawa daga nesa, wadanda ta jibge irinsu a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu