( FAO) ta sanar da cewa an sami karuwar farashin abinci da kaso 2% a duniya
Sanarwar ta kuma ce wannan hauhawar farashin ya shafi rayuwar miliyoyin mutane a duniya.

Bugu kari, sanarwar ta ci gaba da cewa; An sami wannan karuwar ne a cikin watan Nuwamba na wannan shekara,idan aka kwatanta da lokaci irin wannan a shekarar da ta gabata, saboda sauyin yanayi da kuma illar da ya jawo da ake iya ganinta a duniya.

Jean Marie BIADA wanda kwararre ne akan harkokin ci gaba da masana’antu, ya tabbatar da tasirin sauyin yanayin akan hauhawar farashin yanayi.

A kasashe da dama an sami bullar fari da kuma ambaliyar ruwa a wasu kasashen. Kasar Zimbabwe tana daga cikin kasashen da su ke fuskantar karancin abinci a shekarar bana.