Firai Ministan na kasar Malaysia wanda ya gabatar da jawabin bude taron Kualalumpur 2019, ya jaddada cewa; Wajibi ne a kawo karshen yadda ake nuna kyamar musulunci a duniya.

Bugu da kari Mahathir Muhammad ya bayyana fatansa na ganin cewa taron da ake yi a kasar tasa wanda kuma ya sami halartar shugabanni da dama, ya samar da amfani mai girma ga al’ummar musulmin duniya.

Jaridar “Malay Mail” ta yau Alhamis ta buga labarin yadda aka yi bikin bude taro na birnin Kulalampur, ta bayyana cewa; Daga cikin shugabannin da su ka sami halartar taron da kawai shugaban Iran Hassan Rauhani, shugaban Turkiya Rajab Tayyib Urdugan, da kuma sarkin Qatar Tamim Bin Hamad.

Da ya ke gabatar da jawabi a wurin liyafar girmama da ya shiryawa mahalarta taron cewa; Mun shirya wannan taron ne domin jin cewa wajibi ne mu samo hanyoyin kyautata rayuwar al’ummar musulmin duniya.”

Mahathir Muhammad ya kuma yi ishara da cewa; Tare da cewa musulmi ne mafi rinjaye a kasarsa amma kuma suna da tsirarun mabiya addinai daban-daban da su ke rayuwa cikin zaman lafiya.