Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi kira ga kasar Koriya ta arewa (DPRK), ta amince da sake dawowa kan teburin tattaunawa da Amurka kan batun shirin kawar da makaman nukiliya.

A sanarwar da kakakin babban sakataren ya fitar ya ce, Guterres ya sake jaddada bukata ga shugaban Koriya ya amince da shirin wanzar da zaman lafiya da tsaro a zirin Koriyar kuma ya yi aiki tare da bangaren Amurka don ci gaba da tattaunawar bangarorin biyu, in ji Stephane Dujarric, kakakin sakataren MDD.
A jawabin da ya gabatar a taron manema labarai, Dujarric ya ce, hanyar diflomasiyya ce kadai hanya mafi dacewa wajen samar da dauwwamamen zaman lafiya da kawar da makaman nukiliya daga zirin Koriya.

Wakilin dindindin na koriya ta Arewa a MDD, Kim Song, ya fada cikin wata sanarwa a ranar Asabar cewa, a halin yanzu ba su da bukatar yin doguwar tattaunawa da bangaren Amurka, kuma batun kawar da makaman nukiliya tuni an riga an cire shi daga teburin tattaunawa.