TAKARDAR SANARWAR MANEMA LABARAI

Da kakkausar murya muna shelanta tir din mu, da kuma Allah wadai dangane da kalamai na karya da rashin dacewa wadanda Ministan yada labarai, Mista Lai Muhammad ya bayyana a cikin yan kwanakin nan cewa, Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky, ana tsare da shi ne a kan abin da ya kira wai dalili na aikata laifuka ba shaani na addini ba. Tabbas, idan har akwai wanda ya cancanci a tsare a kuma tuhuma da aikata laifuka, to babu shakka kuwa za su kasance manyan mukarraban jamian gwamnatin Muhammadu Buhari ne, wadanda suka kashe sama da mutane dubu daya, yan  Kasa fararen hula
wadanda ba su dauke da makami haka siddan, tare kuma da yi masu kabari na bai-daya a cikin tsakar dare, suka kuma dauki dukkanin matakai na karfin gwamnati domin boye hakikanin gaskiya da kuma kawo cikas, hade da tarnaki wajen ganin an yi adalci a kan lamarin.

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta yi kemadagas ta ki mutunta doka da Oda, tare ma da ci gaba da cutar da yan’uwa Musulmi na Harkar Musulunci a Nijeriya, musamman take masu hakki da yanci da ake ci gaba da yi a kowane lokaci, lamarin da ya zama sananne ga alummar kasa da kasa. Lamarin da ya cancanci gudanar da bincike ga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) da ke birnin Hague. Haka nan kuma, da yawa daga cikin Kungiyoyin kare hakkin BilAdama na ciki da wajen Kasa irin su, Amnasty International, Human Rights Watch da kuma Kungiyar Kare Hakkin BilAdama ta Musulunci, dukkanin su sun gudanar da bincike tare kuma da tattara bayanai na bakin zalunci da aka yi wa yan uwa Musulmi na Harkar Musulunci a Nijeriya da kuma Jagoran ta, bayanan da dukkanin su suka nuna tare da tabbatar da cewa an yi mana wannan zalunci ne saboda fahimtarmu ta addinin Musulunci. Bakin Zalunci da kuma tauye hakkin yan’uwa Musulmi na Harkar Musulunci a Njeriya da ake yi batu ne wanda ya dauki hankalin alummar duniya, musamman batu na yan kwanakin nan da ya fito daga gwamnatin Amurka, yana gaskata cewa babu wata karya da Lai Muhammad zai iya kantarawa wadda za ta iya boye wannan zalunci da gwamnatin Buhari ta aikata kuma take ci gaba da aikatawa.

Ba za iya yaudarar alummar duniya da wadannan kagaggun tuhume-tuhume na karya da ake yi wa Shaikh Zakzaky ba, musamman kasantuwar kimanin mutane dari da ake tuhumar sa da taimakawa wajen aikata laifuka, dukkanin su Kotu da sake su, tare kuma da wanke su daga aikata wani laifi. Haka nan kuma kasantuwar an tuhume shi da laifin aikata su ne bayan an shafe sama da shekaru biyu ana tsare da shi a boye, kuma bayan sama da shekara daya da rabi da babbar Kotu da ke Abuja ta bayar da umurnin sakin sa ba tare da gindaya masa wani sharadi ba, ya isa ya zama sheda wajen nuna cewa gwamnatin Nijeriya tana kame-kame ne wajen neman hujjar ci gaba da tsare shi dindindin.

Kar fa a manta cewa, ba da dadewa ba, shi dai wannan Minista na yada Labarai ya bayyana wa yan Nijeriya cewa Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Zakzaky ana tsare da shi ne domin ba shi kariya, ba ana tsare da shi ba ne domin ya aikata wani laifi. Haka nan kuma, a yunkurinsu na nuna dacewar wannan haramtacciyar tsarewa, Ministan yada labaran, Lai Muhammad shi ne kuma ya bayyana wa yan Nijeriya cewa ana ci gaba da tsare Shaikh Zakzaky ne saboda babu wanda yake so Shaikh zakzaky ya makwabce shi. Mista Lai ne dai wani lokaci a cikin wani shiri
na gidan Talabishin ya bayyana cewa Kotu ba ta da cikakkiyar masaniya kan lamarin tsarewar da suke wa Shaikh Zakzaky, don haka ba za su bi umarnin da ta bayar ba. Duk dai wannan Minista ne ya kuma shirga karya a kan makudan kudin da gwamnati take kashewa wajen ciyar da Shaikh Zakzaky abinci.

Yadda gwamnati ke sauya dalilan ci gaba da tsare Shaikh Zakzaky shi kansa na nuni da cewa da akwai wata manufa ta daban na addini da ake fakewa da shi, lamarin da hatta Mai girma Gabriel Kolawale, Alkalin babbar Kotu da ke Abuja a yayin da yake zartar da hukunci ya tabbatar da shi a inda ya ce, Makirci da kutunguila irin na mafiya yawan Musulmi mabiya Mazhabar Sunnah a kan tsiraru Musulmi mabiya Mazhabar Shia ne babban Ummul habaisin da ya sabbaba wannan hatsaniya wadda ta jaza ci gaba da tsare Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya da kuma ci gaba da cutar da yanuwa Musulmi na Harkar Musulunci a Nijeriya. Wannan batu kuma shi ne matsayar gwamnatin Amurka, don haka babu wani nauin karya, goga bakin fenti ko kuma cutarwa da za ta iya canza wannan batu.

Mu, yan uwa Musulmi na Harkar Musulunci a Nijeriya da kuma Jagoranmu, Shaikh Ibraheem Zakzaky, muna da yancin gudanar da addini, yin taro da kuma bayyana raayi kamar kowane dan Nijeriya, lamurran da gwamnatin Buhari take tauye mana hakki a kansu da kuma azabtar da mu bisa zalunci saboda rikonmu da kuma fahimtarmu ta addini. Babu wata tantama, Shaikh Zakzaky fursuna ne na Imani, ana tsare ne da shi saboda fahimtarsa ta addinin Musulunci.

Don haka muna kira ga daukacin alumma da kada su yi kasa a guiwa wajen nuna kin amincewarsu da kuma kiyayyarsu ga bakin zalunci na gwamnatin Muhammadu Buhari. Ya zama wajibi a taka wannan gwamnatin burki, a kuma dawo da ita bisa turbar mutunta doka da Oda ta hanyar gaggauta sakin Shaikh Zakzaky, ba tare da gindaya
masa wani sharadi ba.

SA HANNU:
IBRAHIM MUSA
SHUGABAN DANDALIN YADA LABARAI NA HARKAR MUSULUNCI A NIJERIYA
23/12/2019
Fassarar Zaharaddeen Sani Malumfashi.