Hukumomin gwamnatin rikon kwarya ta kasar Sudan na kokarin rufe ofisoshin kungiyoyin gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Labnon da Hamas na Falastinu a birnin Khartoum.

Wata kafa ta kusa da gwamnatin rikon kwaryar Sudan ta yi da'awar cewa firai ministan kasar Abdallah Hamduk na kokarin rufe ofisoshin kungiyoyin gwagwarmayar na kasashe waje da suke jerin cikin kungiyoyin da kasar Amurka ta kakabawa takunkumi daga cikinsu akwai kungiyoyin gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Labnon da Hamas ta Palastinu.

Majiyar ta ce gwamnatin Hamduk za ta dauki wannan mataki ne domin ganin ta samun amincewar hukumomin Amurka su tsire kasar Sudan daga cikin jerin kasashen dake taimakawa kungiyoyin 'yan ta'adda da kuma Amurka ta kakabawa takunkumi.

Tun a shekarar 1993 ne kasar Amurka ta sanya kasar Sudan din a jerin kasashen dake taimakawa kungiyoyin 'yan ta'adda a Duniya tare kuma da kakabawa kasar takunkumi.

Bayan kwashe sama da shekaru 15, kasashen Sudan da Amurka sun cimma matsaya na sake meda huldar Diplomasiya a tsakaninsu.