Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Harin Ta'addanci Ya Ci Rayukan Mutane 22 A Kasar Congo


Hukumomin jamhoriyar Dimokaradiyar Congo sun sanar da mutuwar mutane 22 sakamakon harin ta'addanci a gabashin kasar.

Kamfanin dillancin labaran All Afirka ya nakalto hukumomin jamhoriyar Dimokaradiyar Congo na cewa harin ta'addancin da aka kai a tsakiyar kasar wato lardin Oriental ya yi sanadiyar mutuwar mutane 22 da kuma jikkata wasu 18 na daban.

A cewar masu rajin kare hakin bil-adama na kasar daga farkon watan Oktoba zuwa yanzu ,sama da 'yan kasar Congo 150 suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren ta'addanci a kasar.

Gwamnatin kasar Congon ta dora alhakin hare-haren ta'addancin kan gamayar dakarun 'yan tawaye na ADF.

Sama da shekaru 20 kenan da jamhoriyar Dimokaradiyar Congo ke fuskantar hare-hare daga bangaren kungoyin 'yan tawaye dake dauke da makamai.

A bangare guda kuma tashar SABC ta kasar Afirka ta kudu ta bayar da Rahoton cewa kimanin masu hakar ma'adanai 27 ne suka rasa rayukansu sakamokon rubtawar kasa a arewa maso gabashin kasar ta Congo.
Ko a makoni uku da suka gabata ma, zaizayar kasa ta yi sanadiyar salwanta rayukan mutane 41 a birnin Kinshasa fadar milkin kasar ta Congo.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu