Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Hukumar EFCC A Nigeria Ta Rufe Ofishin Jaridar The Sun


Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta rufe gidan jaridar The Sun. saboda laifin satar kudi da yawansu ya kai N7.65 biliyan

Kamfanin na the suna na daga cikin kadarorin tsohon gwamnan jihar Abia Sanata Orji Uzo Kalu da kotu ta yanke wa hukuncin daurin shekara 12 a gidan kaso saboda kama shi da laifin yin zambar kudi har naira biliyan 7.65.

Kakakin hukumar EFCC Wilson Uwujaren ya fadi cewa an rufe gidan jaridar ta the sun ne bayan umurnin da babbar kotun da ke zamanta a birnin Legas, na rufe dukkan kadarorin da tsohon gwamnan ya mallaka sannan a mika su ga gwamantin kasar.

A wata sanarwar da kakakin hukumar ya fitar, Wilson Uwujaren ya ce hukumar EFCC na sanya alamomi tare da rufe dukkan kadarorin tsohon gwamnan ne domin kauce wa duk wani yunkurin karkatar da su ta wata hanya.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu