Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

INA BUKATAR SAKE YIN AURE:- IBB

MACE TA GARI NIKE NEMA...
-KADUNA PRESS

Ina matukar jin kadaici wasu lokutan, daya daga cikin manya-manyan tsare-tsare na a sabuwar shekara mai zuwa shine na samarwa da kaina abokiyar zama.
Ammanfa ba kawai mace nike nema ba, a'a ina neman mace ta gari ne.
Tsohon shugaban kasar Nigeria a mulkin soji General Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya wallafa a shafinsa na tuwita ranar lahadi 29/12/2019.

Wannan rubutun dai ya biyo bayan da al'umma ke rade-radin cewa ya bar duniya ne, sai wasu manema labarai suka kai masa ziyara domin ganewa idonsu sannan kuma suji daga bakinsa ko kuma na ahalinsa.
IBB dai ya shiga halin gwauranta ne tun a watan disanbar dubu biyu da tara 2009 a lokacin da mai dakinsa Maryam Muhammad King (Maryam Babangida) ta cika.
Malama Maryam King dai ta mutu ta barshi da 'yaya hudu Muhammad, Aminu, Aisha da Halima.
-J.S.A
-KNPRSCD 06
-30/12/2019.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu