Ministocin harkokin waje na kasashen Iran da Rasha sun bayyana cewa kasashen yamma, musamman Amurka suna kokarin tabbatar da cewa zaman lafiya bai dawo a yankin gabasa ta tsakiya ba.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto manya-manyan jami’an diblomasiyyar kasashen biyu suna fadar haka a jiya Litinin a birnin Mosco.

Amurka wacce ta ci dubban kilomita daga kasarta zuwa wannan yankin, tana zubar da jinin mutanen kasashen Iraqi da Syria da sunan kare kanta, inji Mohammad Jawad Zarif a ganawarsa da Sergei Lavrov takwaransa na kasar Rasha a birnin Mosco.

Zarif ya yi ishara da hare-haren da sojojin Amurka suka kai kan dakarun “Hashdus-shaabi” na kasar Iraqi a a ranar jumma’an da ta gabata a matsayin misali na zubar da jinin mutane ba tare da wani dalili ba.

Kamfanin dillancin labaran Sputnic na kasar Rasha ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Sergei Lavrov ya na cewa “muna kallon wasu kasashen yamma suna ruruta wutan fitina da gangan a yankin gabas ta tsakiya”.