Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Iran Ta Bude Bangare Na Biyu Na cibiyar Nukiliya Ta Arak


Ajjiya litinin ne shugaban hukumar kula da makamashin nukiliyar Iran Ali Akbar Salihi ya yi ran gadi da yan jaridu a garin

Khundab da ke tsakar kasar Iran domin gane wa idonsu irin nau’rorin ta ke da su da kuma yadda kwararrun masana na kasar suka gudanar da ayyukansu.

Kuma wannan yazo ne a lokacin bukin bude bangaren na biyu na ayyukan tace ruwa mai kauri a cibyar Nukiliyar da ke birnin Araka da ya gunada a yau, da hakan ya kawo karshen jinkirin da Iran ta yi samakon yarjejeniyar da aka rattaba hannun akai tsakaninta da kasahen turai kan shirinta na Nukiliya.

Bisa yarjejeniyar da aka cimma Iran ta amince ta cire naurar da ake amfani da ta a cibiyar ta Arak tare da maye gurbinta da wanda bangaren da aka cimma yarneniyar za su bada domin ci gaba da ayyukanta domin samar da magunguna, sai dai shiru kake ji daga bangaren kasahen turan.

Tuni dai Iran ta mayar da martani game da ficewar da Amruka ta yi daga cikin Yarjejeniyar da kasa cika alkwawuran da sauran kasashen turai suka dauka, inda ta dakatar da aiki da wasu yarjejeniyoyin da aka cimma matsaya akai har sai bangaren kasashen turai sun yi aiki da na su bangaren a aikace.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu