Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Iran Ta Musanta Rahoton Reuters Kan Adadin Wadanda Suka Mutu A Zanga zanga


Shugaban cibiyar watsa labarai na Majalisar Koli ta Tsaron Kasar Iran yayi watsi da kuma musanta wani rahoto da kamfanin dillancin labaran Reuters ya watsa inda ya ce mutanen da suka rasa rayukansu a rikicin baya-bayan nan da ya faru a Iran sakamakon karin farashin man fetur sun kai mutane 1500.

Malam Alireza Zarifian Yeganeh ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran inda ya ce irin wannan ikirarin wani nau’i ne na yaki na kwakwalwa wanda ba shi da wata kima.

Malam Yeganeh ya ci gaba da cewa wannan rahoto na kamfanin dillancin labaran na Reuters wani lamari ne maras kima shin a fagen tsaro ne ko kuma a fagen aikin jarida ne, wanda hakan kuma zai kara zubar da mutumcin kafar watsa labaran ne wanda tun da jimawa yake tangal-tangal.

A wani rahoto da kamfanin Reuters din ya buga a jiya Litinin ya ce kimanin mutane 1,500 ne suka rasa rayukansu yayin rikicin ciki kuwa har da yara 15 da kuma mata kimanin 400 da kuma wasu jami’an tsaro, yana mai cewa wai wasu jami’an ma’aikatar cikin gidan Iran ne suka ba shi wannan labarin ba tare da yayi karin bayani ba.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu