Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Iran Ta Yi Watsi Da Zargin Da Amurka Ta Yi Mata Na Taimaka Wa Kungiyar Taliban


Babban sakatare majlisar kolin tsaron kasa Ali Shamkhani da yake jawabi a wajen wani taro a da aka gudanar kan tabbatar da tsaro a yankin ya yi watsi da zargin da Amurka ta yi wa Iran na cewa tana taimaka wa kungiyar Taliban da kudi da makamai kuma bayar da horo a kasar Afganistan domin ta yaki dakarun mamaya na Amurka dake kasar. Ya kara da cewa wannan zargin yayi hannun riga da manufofin siyasar Iran.

Har ila yau ya kara da cewa Iran tana adawa da tattaunawar dake gudana tsakanin Amurka da kungiyar Taliban saboda duk wani mataki da ake son dauka ba tare da sa hannun gwamnatin Afghanistan ba baban kuskure ne kuma haka ba za ta cimma ruwa ba.

Daga karshe Ali Shamkhani ya fadi game da kasancewa yan kungyar ta’adadncin ta Daesh a kasar Afghanistan cewa a ajiye sansanin kungiyar kasar dake Kudu masu Gabashin Asiya wani yunkurin na haifar da fitinin da rashin tsaro a iyakokin dake tsakanin kasashen Iran Chaina da kuma kasar Rasha.

Daga karshe ya yi kira ga dukkan kasashen yankin da su hada kai wajen yaki da abin da ya kira mummunar manufar Amurka a yankin gabas ta tsakiya , kana ya soki Amurka da sauran kawayenta na turai wajen kasa dawo da zaman lafiya a kasar Afghnaistan.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu