Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Iran : Takunkumin Amurka, Take Hakkin Dan Adam Ne


Kakakin ma'aikatar harakokin wajen Iran ya ce takunkumin da kasar Amurka ta kakabawa kasar, babban misali ne da aikata laifi kan bil-adama da kuma ta'addancin tattalin arziki.

Yayin da yake gabatar da taron manema labarai a birnin Tabriz dake arewa maso yammacin kasar, kakakin ma'aikatar harakokin wajen Iran sayyid Abas Musavi ya yi watsi da ikrarin da kasar Amurka ke yi na cewa ba ta kakabawa bangaren abinci da magani na kasar Iran takunkumi ba, inda ya cewa duk wani kamfani na cikin kasar ta Iran dake mu'amalar samar da abinci gami da magani na fuskantar matsalar safarar kudade a bankuna sakamakon takunkumin da kasar Amurka ta kakabawa kasar.

Musavi ya ce takunkumin da kasar Amurka ta kakabawa Iran ya sabawa dukkanin dokokin kare hakin bil-adama da na kasa da kasa.

A bangare guda Musavi ya yi isharar kan ziyarar da shugaba Rouhani ke shirin kaiwa kasar Japon, inda ya ce hukumomin kasar na Japon da kyakkyar niya sun bayar da shawarar rage rikici tsakanin dake tsakanin kasashen Iran da Amurka , kuma fatanmu shi ne ziyarar ta shugaba Rouhani zai kai kasar ta Japon ta yi sanadiyar cimma matsaya mai kyau tsakanin bangarorin biyu.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu