Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Ivory Coast Ta Fitar Da Sammacin Kama Dan Takaran Shugabancin Kasar, Guillaume Soro


Gwamnatin kasar Ivory Coast ta fitar da sammacin kama tsohon madugun ‘yan tawaye kana kuma daya daga cikin ‘yan takaran shugabancin kasar,
Guillaume Soro, lamarin da ya sanya Soro dakatar da shirin dawowarsa gida.

Babban mai shigar da kara na kasar Ivory Coast din Richard Adou ne ya bayyana hakan inda ya ce tuni aka fitar da sammacin kamo Soron saboda zargin barazana ga tsaron kasa, karbar kayayyakin sata da kuma fasa kwabrin kudade.

A jiya ne dai aka tsayar Soro din zai dawo gida daga birnin Paris na kasar Faransa inda yake zaune saboda tsaron lafiyarsa.

A jiyan dai an yi arangama tsakanin jami’an tsaro da magoya bayan Soron wanda a baya ya taba zama madugun ‘yan tawayen kasar a yayin rikici da ya barke a kasar a shekara da yayi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 3000.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu