Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Jadawalin Zagaye Na Gaba Na Karawar Gasar Cin Kofin Nahiyar Turai Na Shekarar 2019/20.UEFA CHAMPIONS LEAGUE DRAWS 2019/20

Kungiyoyin da su ka samu kai wa ga nasara sun san abokan karawarsu a halin yanzu.

1. Real Madrid v Manchester City
Manchester City za ta kara da kungiyar Real Madrid a wannan zagaye na kungiyoyi 16 da su ka rage. Pep Guardiola ya fito ne a matsayin na farko a rukuninsa. Wannan wasa zai yi budu sosai.

2. Chelsea v Bayern Munich
Wani wasa da jama’a za su kosa a buga shi ne na Chelsea da Bayern. Chelsea sun iya fitowa ne daga rukunin farko da kyar a makon jiya. Bayern kuma sun yi nasara a duka wasanninsu.

3. Dortmund v PSG
Kungiyar Dortmund da ta fito tare da Barcelona za ta fafata da Zakarun kasar Faransa watau PSG a sabuwar shekara. PSG kuma ta sha gaban Real Madrid a teburin rukunin farko a kakar bana.

4. Liverpool v Atletico Madrid
Zakarun bana, Liverpool za su fara kare kambunsu ne a wajen Atletico Madrid wanda su ka biyo Juventus a baya a rukuninsu. Wannan wasa ya na cikin masu ban kayen da ake sa ran kallo.

Ga cikakken hadin da hukumar kwallon kafa ta Turai ta UEFA ta yi a ranar 16 ga Watan Disamban 2019.
Borussia Dortmund da Paris Saint-Germain

Real Madrid da Manchester City

Atalanta da Valencia

Atletico Madrid da Liverpool

Chelsea da Bayern Munich

Lyons da Juventus

Tottenham da RB Leipzig

Napoli da Barcelona

Yi hasashe ya ku ke ganin wasannin nan za su kasance? 

Post a Comment

0 Comments

Close Menu