Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Jagoran Musulunci Na Iran Ya bukaci A Yi Mua’amalar Jin Kai Ta Musulunci Da Wadanda Suka Ta Da TarzomaWannan kiran ya zo ne yayin mayar da martani game da rohoton da sakataren Kwamitin koli na tsaron kasar Ali Shamkhani ya mika wa jagoran da ya shafi mu’amala da wadanda suka jikkata a lokacin tarzomar da ta ta shi a baya- bayan nan, bayan sanar da karin kudin man fetur da gwamnatin kasar ta yi.

Jagoran musulunci na kasar Iran Ayatullahi sayyid Ali khamna’i ya nuna gamsuwa da shawarwarin,inda ya bukaci a fara aiki da ita cikin gaggawa. Kuma jin kai irin na Musulunci ya zamo shi ne akan gaba wajen mu’amala da wadanda ake tsare da su duk girman zargin da ake musu na aikata laifi.

Har ila yau ya zo a cikin rahoton cewa duk mutanen gari da suka rasu da ba su da hannun wajen tayar da tarzomar suna matsayin shaidai ne, kuma za’a ci gaba da kulawa da iyalansu karkashin cibiyar kula da shahidai ta kasa.

Su ma wadanda suka mutu sakamakon arangma da makami da jami’an tsaro za’a gudanar da bincike game da abubuwan da iyalensu suka aikata a baya, tare da tantance tsakaninsu da wanda ya aikata laifin, domin daukar mataken da suka dace akansu. Sai dai wadanda aka tabbatar da hannunsu wajen aikata mummunan aiki, jagoran ya bukaci a yi la’akarin da jin kan musulunci wajen mu’amala da su.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu