Amurka ta janye jakadanta daga kasar Zambia, bayan shugaban kasar Edgar Lungu, ya ce jakadan na AMurka ba shi da wata kima a Lusaka babban birnin kasar.

Zambia ta kori jakadan na Amurka ne, bayan da ya yi tir da hukuncin zama gidan yarin da aka yanke wa wasu masu auren jinsi guda a kasar.

Shi dai jakadan na Amurka, Daniel Foote, ya bayyana a wata guda da ya gabata, jin takaicinsa kan hukuncin da aka yanke mutanen, tare da bukatar mahukuntan na Zambia sun sake duba dokokin kasar wadanda ya ce akwai rashin adalci a cikinsu, lamarin da bai yi wa mahukuntan kasar a sahun gaba Shugaban Edgar Lungu dadi ba.

Shugaba Lungu ya daganta kalaman jakadan na Amurka da cewa suna yi wa addinin Krista karan-tsaye.