Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Jami’an SSS a Nigeria Sun Binciki Sowere Kan Dagantakarsa Da Harkar Musulunci A Najeriya.


Wata mjiya da ke bibiyar halin da mawallafin jaridar Sahara reporters ke ciki Omoyele Sowere ta bayyana cewa : Jami’an tsaro na farin kaya SSS sun tambaye shi game da alaka kud da kud da ke tsakaninsa da kungiyar ta’adda ta Boko Haram da kungiyar IPOBI mai fafutukar kafa kasar Biafara da kuma Harkar msulunci a Nigeria da sauran kungiyoyin da aka haramta, sai dai ya musanta zargin duk wata dangantaka tsakaninsa da wadannan kungiyoyi.

Ita dai kungiyar boko Haram an hamarta ta ne a lokacin gwamnatin Good lock Jonathan, kafin daga bisani a watan Nuwamba shekara ta 2013 kasar Amurka ta sanya ta cikin jerin kungiyar yan ta’adda ta kasa da kasa.

Masana na bayyana cewa wadannan tamabayoyin na nuna cewa akwai alamun jami’an za su bullo da wasu sabbin
tuhume –tuhume ne kan dan rajin kare
hakkin dan adam din da ake ganin za ta
gabatar a gaban koto a nan gaba, kuma ana ci gaba da tsare shi ne da zargin ta’adanci da ci amanar kasa, zargin da tuni ya Musanta, kuma har yanzu ba’a sake shi ba duk da belinsa da kotu ta bayar

Post a Comment

0 Comments

Close Menu