Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Jaridar Punch: Daga Yanzu Za Mu Fara Kira Shugaba Muhammadu Buhari Da Sunan Dan Kama-Karya


A fitowarta ta jiya Laraba, jaridar ta “Punch” da ake bugawa a Najeriya, ta sanar da cewa: Domin nuna kin amincewa da mulkin danniya mai salo irin na soja, daga yanzu dukkanin jaridunmu za su rika hada sunan Buhari da mukaminsa na soja, Manjo Janar, gwmanatinsa kuma ta kama-karya har zuwa lokacin da za su koma aiki da doka.”

Daga cikin dalilan da jaridar ta ambata na daukar wannan matakin akan shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatinsa da akwai kama dan gwgawarmayar nan Omoyele Sowore mai buga jaridar Sahara Reporters da jami’an asiri na SSS su ka yi a cikin kotu, da kuma kokarin rufe bakin al’ummar kasar da hana su tofa albarkacin bakinsu a hanyoyin sadarwa na al’umma.

Bugu da kari, jaridar ta Punch ta ambaci yadda gwmanatin tarayyar kasar ta ki sakin jagoran harkar musulunci ta Kasar, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, da kuma Sambo Dasuki duk da cewa kotuna sun bayar da umarni a sake su.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu