Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Kai Mahaifana Kurkuku, Jefa Su A Cikin Mugun Hatsari Ne_Mohammed Zakzaky


Ina rubuta wannan ne a matsayin matakin nuna rashin amincewa ta da muzgunawa mahaifina, Shaikh Ibraheem el-Zakzaky, da kuma mahaifiyata Zeenah el-Zakzaky da hukumomin Nijeriya suke ci gaba da yi.

Gaggawar mayar da mahaifana gidan kurkukun Kaduna daga inda hukumar tsaro ta DSS take tsare da su, ya sake jefa rayuwarsu a cikin mugun hatsari.

Sanin kowa ne yanayin gidajen kurkukun Nijeriya kadai ya isa ya jefa mai cikakkiyar lafiya cikin muguwar rashin lafiya, balle kuwa wanda yake fama da rashin lafiya.

Kamar yadda kowa ya san cewa mahaifina ya rasa ido daya, sakamakon harbinshi da akayi a lokacin kisan kiyashin Zariya, wanda ya afku a cikin watan Disamban shekarar 2015, sannan ya fuskancin matsalar bugun jini a lokacin da yake tsare a wajen hukumar DSS, ba sau daya ba, ba sau biyu ba, wani kwararren likita mai zaman kanshi ya bayyana cewa ya na ma fuskantar barazanar mutuwa a kowanni lokaci.

Haka ma mahaifiyata, tana fama da matsannanciyar rashin lafiya, tana da hawan jini, sannan bata iya tafiya ma gaba daya, saboda tana fama da ciwon gwiwa, dadin dadawa akwai harsashi a makale a bayanta kusa da bargo.

Sannan ina kara nuna rashin amincewa ta da hana ni ganin mahaifana, sun hana mu ganinsu, lokacin da muka je ni da wasu daga cikin danginmu, da kuma lauyoyinmu, duk da kotu ta bamu damar ziyartarsu.

Wannan ya sabawa tsarin dokar gidan kurkuku, kuma kari ne akan matakan take hakkin ‘dan adam, akan duk matakan da aka dauka a kan mahaifana a baya.

Kamar duk wani dan kasa, yakamata ne a yi mu’amala da mahaifana kamar yadda dokar kasa ta tanada, amma a kansu abun ba haka yake ba, anyi watsi da tanadin dokar kasa wajen yin mu’amala da su.

Abinda ya kaimu gidan kurkuku yau, ni da lauyoyinmu shine mu duba lafiyarsu, amma muna ji muna gani aka hana mu ganinsu, duk da mun je a daidai lokacin da ake ziyara. Wannan shine mataki na baya baya na bakin zaluncin da ake yi musu kullum.

Mohammed Ibraheem Zakzaky
9/12/2019.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu