Kamfanin kera jiragen sama na Amurka Boeing ya sanar da dakatar da kera jiragansa samfarin 737 MAX, sakamakon sakamakon tsaka mai wuya da ya tsunduma a karon farko cikin tarihi.

A watan Maris na shekara nan ne aka haramta tashi da saukar jiragen na Boeing samfarin 737 Max, bayan hatsarin irin jiragen guda biyu.

Wannan shi ne karo na farko a cikin shekaru 20 da kamfanin ya taba fuskantar irin hakan na dakatar da kera jiragensa.
Matakin dakatar da kera jiragen wanda aka shafe kwanabi biyu ana tattaunawa kafin daukansa zai fara aiki ne daga watan Janairu na shekara 2020 mai shirin kamawa.

Dama dai adadin jiragen da kamfanin ke kerawa a cikin wata guda ya ragu daga 58 zuwa 48.

A makon da ya gabata ne hukumar kula da sufirin jiragen sama ta Amurka, ta ki amince bada damar dawo da jiragen samfarin 737 max daga aiki.

A baya baya nan an gudanar da gwaje gwaje har sai biyu kan jiragen, saiai hukumar ta (FAA), ta ce hakan bai wadatar ba, duba da hadarurukan da samfarin jiragen sukayi a kasa da watanni biyar, wanda kuma ya yi sanadin mutuwar fasinjoji 346.