Sarkin kasar Qatar Sheikh Tamim Bin Hamd al’ Thani ya sanar da yin watsi da gayyatar da kasar Saudiyya ta yi masa na halartar taron shekara -shekara karo na 40 na kashean yankin tekun fasha a birnin Riyad na kasar Saudiya.

Rashin halartar Sheikh Tamim zuwa wajen taron ya kara sanyaya gwiwa game da fatan da ake da shi na yin sulhu tsakanin kasashen guda biyu, bayan da rikicin diplomasiya ya kunno kai tsakaninsu kusan watanni 30 ke nan.

A shekara ta 2017 ne kasashen Saudiya da Masar da Haddiyar Daular Larabar su ka kakabawa kasar ta Qatar takunkumi ta kasa da sama da ruwa da hana ta shigo da kayayyaki cikin kasar, bayan da suka zarge ta da taimakawa ta’addanci , zargin da tuni mahukumtan na Doha suka musanta.

Kawancen da Saudiya ke jagoranta ya ba wa kasar Qatar wa’adi na ta cika wasu sharuuda da ya gabatar mata ko kuma ta fuskanci abin da zai biyo baya. Sai dai gwamatin Doha ta yi watsi da sharuddan kana ta jaddada cewa ba za ta yi watsi da yancinta na kare manufofin siyasar kasarta ba.