Kasashe mambobin kungiyar shugabannin Afirka da Caribbean da Fasifik ko (ACP) a takaice, sun fara gudanar da taron su karo na 9 a birnin Nairobin kasar Kenya, inda suka yi kira da a dauki matakan bunkasa tsarin cudanyar cinikayya bisa daidaito, don samar da ci gaba na bai daya, da zaman lafiya tsakanin kasashe masu tasowa.

Da yake jawabi yayin bikin bude taron na jiya Litinin, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, wanda kuma a wannan karo ya karbi ragamar jagorancin kungiyar ta (ACP) na tsawon shekaru 3, ya ce ya kamata a karfafa dokokin cudanyar sassan duniya, ta yadda hakan zai magance kalubale da dama da ake fuskanta, ciki hadda talauci, da tashe tashen hankula, da tsattsauran ra'ayi, da batun sauyin yanayi.

A nasa jawabi kuwa, babban sakataren kungiyar Patrick Gomes, cewa ya yi taron na birnin Nairobi, ya samar da wata hanya ta jaddada burin kasashe masu tasowa, game da amfana daga damammakin dake akwai na ciyar da kan su gaba, da martaba doka da oda, da inganta tsarin cudanyar kasa da kasa, da samar da kyakkyawan jagoranci, da zaman lafiya da lumana.