Turkiyya ta yi watsi da sanarwar da Saudiyya ta yi na cewa ta yanke hukuncin kisa kan wasu mutane biyar da ake zargi da kashe dan jaridan kasar Jamal Khashoggi tana mai bayyana shari’ar a matsayin wani wasa da hankali kawai.

A wani sakon da ya watsa a shafinsa na Twitter, daya daga cikin masu ba wa shugaban kasar Turkiyyan Rajab Tayyib Erdogan shawara, Fahrettin Altin ya ce hukumcin da aka zartar din nesa ba kusa ba yayi nesa da abin da kasar Turkiya da ma sauran kasashen duniya suke fatan gani.

Jami’in ya ci gaba da cewa: Saudiyya ta fitar da wani hukunci na wasan yara bayan watanni na shari’ar sirri kan kisan gillan da aka yi wa Jamal Khashoggi, yana mai cewa: wadanda suka turo makasan a cikin jirgin sama zuwa Turkiyya sannan kuma suka aiwatar da kisan suna nan suna yawonsu.

A shekaran jiya ne gwamnatin Saudiyya ta sanar da cewa ta zartar da hukuncin kisa a kan wasu mutane 5 da ta ce su ne suka kashe Jamal Khashoggin a ofishin jakadancinta da ke Turkiyya, lamarin da bangarori daban-daban na duniya suke ci gaba da sanya shakku cikin lamarin bisa la’akari da yadda aka wanke manyan jami’an Saudiyya na kurkusa da Yarima mai jiran gado na kasar Muhammad Bn Salman da ake zargi da hannu cikin kisan gillan.