Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Kawancen Saudiya Ya Tsananta Kai Hare-Hare A Lardin Hudaida


Sojojin hayar Saudiya sun tsananta kai hare-hare a yankunan dake lardin Hudaida na yammacin kasar Yemen.

Tashar talabijin din Al-hudaida mallakin kasar Yemen ta habarta cewa a wannan Talata sojojin hanyar Saudiya sun kai hare-haren wuce gona da iri a yankunan Duraihamy da Al-Tahita dake lardin Hudaida, lamarin da ya janyo hasara mai yawa ga gidajen fararen hula.

A ranar 18 Dicembar shekarar 2018 din da ta gabata ce tawagar biranan Sana'a da na Riyad suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a kasar Swidden, amma daga wannan lokacin zuwa yanzu kawancen saudiyar sun karya wannan yarjejeniya so da dama.

Yayin da yake ishara kan makircin siyasa na Saudiya mai bawa shugaban kwamitin koli na siyasar kasar Yemen Ahmad Hajar shawar ya ce kawancen saudiya ba sa bukatar sulhu da dawo da tsaro a kasar Yemen, abinda suke so kawai kasarsu ta kasance cikin zaman lafiya ban da kasar yemen, lamarin da ba za mu amince da shi ba, matukar dai suna son zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasarsu, to dole ma kasar ta Yemen ta samu tsaro da kwanciyar hankali.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu