Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

KHATAMAR MAULUDIN MANZO (S.A.W) A DA'IRAR KADUNA....
-KADUNA PRESS.

A yau lahadi   08-12-2019 dai dai ga 10 Rabi Al Saani 1441, Da'irar kaduna ta gudanar da Khatama Mauldin Manzon Allah (s.a.w.a). Kamar yadda a ka saba duk shekara bayan kammala Mauldai halkoki sai a gudanar da taron Khatama, sannan a raba kyautukan da na daya zuwa na uku ga wandan da suka fi kwazo wajen shirya Mauldin.

Sheikh Ibrahim Akil ne ya gabatar da jawabi, bayan farawa da addu'a sai ya yi godiya ga Allah, sannan ya fara jawabi, malamin ya tabo fannonin da dama, inda ya fara da da cewa: babu wata halitta da za tayi dai dai da ta Manzon Allah (s.a.w.a) balanta ya fita, kowace dabi'a ka dauko matukar sunan ta kyakkyawan zaka ga Manzon Allah ne a kan gaba. 

Allah Madaukakin Sarki ya na so aiko wannan Manzon ne ga ne ya zama rahama ga dukkan talikai, malamin ya ta bo janibobi da dama game da rayuwar Manzon Allah dabi'u da jarabawowin da ya fuskanta.

Sannan ya kara da cewa: ba shakka abin da ya faru da Manzon Allah (s.a.w.a), shine ya faru da da dan fodiyo, shi ne kuma ya faru da Imam Khomeini, muma a wannan nahiyar Allah ya so ya dube mu da rahamar sa, a lokacin da mun manta sakon Allah da yawa sun dauka hausa ne Alamin Musulunci, ta yadda in baka jin hausa wani na iya bige ka a rikicin kabilanci, muma muna kyautata zaton Allah ya so ya lullube mu da rahamar sa sai ya tada mana mai kira a bi Allah, wato Sheikh Zakzaky (H).

Sheikh Ibrahim Akil ya kara da da cewa: Lallai I Tarihin Manzon Allah ba abun da za a ji a manta bane, don kullum tarihi ya na maimaita kansa ne, donka karda ka manta da tarihi ka, tarihinka shine kai, ko ba komai ya kamata mu san tarihin Annabi (s.a.w.a) mukuma din ga kwatantasu da wannan zamanin. Dan haka duk lokacin da Allah ya so yin rahama ga talikai yana gwama musu abubu biyu, wato shiriya da mai shirya tawagar. Haka dai malamin ya ta tabo fannonin da dama.

Bayan kammala jawabai sa sai wakilin yan uwa na kaduna Malam Aliyu Tirmiz ya yi ta'aliki. Sheikh Tirmidhiy ya tsinto wasu daga cikin maganganun Malam Akil ya fadada bayanai akai, sannan kuma yakara da wasu bayanai akan lamarin.

Ba a karkare taron ba sai da aka raba kyautuka ga zakarun gasar maulud din kyaututtukansu daga na daya zuwa na uku.
A lokaci guda kuma a wannan ranar ne ake gabatar da gasar faretin yara 'yan Fudiyyoyi da makarantun islamiyyoyi.
'Yan uwan sun gabatar da taron ne a yankin kadaure dake cikin jihar kadunan Nigeria.

Halkar data cinyye gasar a matsayin na uku itace halkar Rasulul akram (T/wada da kewaye).

Halkar Imam Hussaini tana biye da ita a matsayi na biyu da maki saba'in inda ta kerewa sakonta da tazarar ranin maki.
Halkar data lashe gasar ta zarce ta kere ko wacce itace Halkar Ameerul mumineen a matsayin wacce tayi ta daya.

Sannan aka yanka alkaki aka raba walima aka yi addu'a aka sallami kowa.


-Jabeer Bin Said Al'ansariy.
-Kaduna Press.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu