Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

KISAN KIYASHIN DA GWAMNATIN BUHARI TAYI A ZARIA ABUNE DA TARIHIN DAN ADAM BA ZAI MANTA DA SHI BA....Da sunan Allah mai murkushe azzalumai Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halitta Muhammad dan Abdullahi da iyalansa tsarkaka.

A rana mai kamar ta yau ne 12 ga watan 12 shekara 2015, wanda yayi daidai ga watan Rabi'ul Auwal 1437 Hijira. Kwatsam ba za to ba tsan mani da misalin karfe 12 na rana shugaban sojojin Najeriya Yusuf Tukur Burtai, ya jagoranci sojojin zuwa garin Zaria karkashin mulkin 

gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, suka kai harin ta’addanci a nan garin Zaria a kan Muklisin bawa mai son kawo gyara a cikin al'umma wato Sheikh Ibrahim Bin Yakub Zakzaky (H).

Sojojin Najeriya sunyi wannan ta'addancin ne bisa karyar an tare wa shugaban su hanya, Mejo Janar Tukur Burtai, sun kashe dimbim almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) a wurare uku da suka datse su ka killace su, wato Hussainiyyah Baqiyyatullah da ke 1 a kan titin sokoto road, da gidan Jagoran Harkar Musulunci A Najeriya Sheikh Ibraheem Zakzaky da ke Uguwar Gyallesu a nan cikin garin Zaria, da kuma Film Village da ke nan kauyen Danbo a bayan garin Zaria.

Wannan kashe-karshen ta'addancin da rundunar sojojin Najeriya suka aiwatar sunyi sunyi shi ne cikin kwana biyu yini uku, ba dare ba rana duniya na kallo, (Asabar zuwa Litinin) sun kashe sama da dubu, maza da mata yara da manya wadanda basu da ko allura bare Makami, sai carbin salati da kabbara da suke yi, sun kashe matan aure da yawa wasun su ma da juna biyu (ciki) hai huwa ko yau ko gobe, sun kashe yan mata sama da 70 wadanda suke makarantu sakandari da jami'o'i, sun kashe tsofaffi yan sama da shekaru 70 da haihuwa, kuma sun kashe dimbin Matasa da ke karatun digiri a jami'o'i daban-daban cikin Najeriya.

Sun Kashe iyali baki dayansu, (mata da miji, da yayan su), haka kuma suka kashe ma wani uba da yayan sa hudu, dukkanin su yan jami'a ne, sun kashe wa wani bawan Allah hazika yaya mata uku da jikar sa daya da surikin sa, sun kashe wa wata baiwar Allah yayan ta shida da mijin ta da wasu yan uwan ta. 

A yayin wannan ta'addanci na sojojin Najeriya saboda tsabar kan mai uwa dawabi wata baiwar Allah mai ciki ta haihu saboda firgici da Matsin, haka sojoji suka zo suka cin mata suka kashe ta, tare da jinkirin ta, ba tare da ya sha nonon Mahaifiyar sa ba.

Sun harbawa gidan Sheikh Zakzaky gurneti ya kamata da wuta, suka shiga gidan suka dinga harbin muta ne suna jefa su cikin wuta da ransu, majin yatan da ke cikin gidan Harisawa jikin gida Sheikh Zakzaky suka zuba musu fetur suka kona su kurmus.

A wannan Waki'ar an rasa manyan almajiran Sheikh Zakzaky wanda haryanzu ba musan inda sojojin Najeriya suka kai su ba, irin su sheikh Muhammad Mahmud Turi, Sheikh Muktar Sahabi Kaduna, Sheikh Mustafa Lawal Potiskum, Malam Muhammad Kabir Al-Kanawy, Malam Muhammad Auwal Iyal Zaria, Da kuma Dr Mustafa Sa'id, Malam Ibrahim Usman, da sauran su....

Sun Kashe yayan Sheikh Zakyzaky (H) guda uku dukkanin su maza, tattare da cewa shekara guda baya sun wasu ukun wadanda dukkan su suna karatu ne a jami'o'i kasashen waje, sannan sun kashe dan yayan sa, mai suna shamsudin, San sun kashe yayar Sheikh Zakzaky mai suna Goggo Fatima sun kona ta ne da ranta ta kone kurmus.

Sannan Sun isa ga Sheikh Zakzaky (H) da iyalan sa da ke fake a cikin wani dan karamin daki, suka bude musu wuta, in suka harbi matar sa Malam Zeenatuddeen a wurare da dama a jikin ta, suka harbi Sheikh Zakzaky (H) a makasan jikin sa, suka kashe ragowar da ke tare da shi, face yan matan da Allah ya tseratar. Suka kama matan aure da yan mata suka kai su barikin sojoji suka dinga wulaknta su, suka cire musu hijabi suna zuba musu ruwa, suna tayi masu izgilanci iri iri, suka wulaknta gawar wakin da suka kashe, suka bawa mutanen gari damar sace Wayoyin su, zobe, kudaden su, tufafin su.

Sannan sun kashe mutane da dama a shingayen binciken da suka saka, musamman wandan da suka gani da bakin kaya, a irin haka sun kashe mutanen da ba yan Harka Islamiyya ba, da dama. Sannan sun kama daruruwan almajiran Sheikh Zakzaky (H) suka ciga da azabtar da su, ga rauhanin Harshashi a jikin su, sannan suka kai wasu gidan yarin kaduna, wasu kuma har yau ba a San ina suka kai su ba.

Bayan sun gama kisan suka tattara gawarwakin suka kai wasu ungwar Mando nan cikin garin Kaduna suka kato rani suka zuba mata, da maza, da yara, da jarirai, kabarin bai daya (mass grave) ba tare da an musu Sallah ba, ko likafani ba, hasali ma wasu da ran su, sannan suka kai wasu wajen ikon su suka rufe su.

Sun raunata yan uwa Almajiran Sheikh Zakzaky da yawa, wanda sai da a ka fitar da wasu kasashen waje don yi masu magani, wasu sun na kasa, sun rasa gabobin jikin su, wasu gaba daya fatar jikin su ya kone, wasu kuma sun na kasa.

A wannan ta'addanci da sojojin Najeriya tayi sun kashe mutane sama da dubu (1000+). Sun maida mata 550 Zaurawa. Sun mai da yara sama da 1300 marayu. Sun sa dangi sama da 4000 cikin garari, kewa da kadaicin a halin su, sun durkusar da Iyaye dawa saboda kashe masu tai maka musu.

Duk da wannan ta'addaci da sojojin Najeriya suka yi bai ishe su ba, bisa taimakon gwamnatin jihar Kaduna sun bi duk wani waje mallakar harkar musulunci a najeriya sun rusa shi. Hatta kaburbura ba su bari ba sai da suka rusa, sannan suka je makwancin mahaifan Sheikh Zakzaky suka rusa.

Duk wannan abubuwan da muka kawo sun faru ne cikin mako guda kacal, daga ranar 12-12-2015 zu ranar 17-12-2015.

Sannan har yanzu suna ciga ba da tsare Sheikh Zakzaky (H) da iyalin sa, da Almajiransa, cikin rashin lafiya mai tsanani. A gidan kurkukun kaduna.

Muna addu'a Allah ya tsine wa duk wani mai hannu a wannan ta'addancin, da wanda suka tai maka musu ko da da murna ne, Allah ya hana musu walwalar duniya da lahira. Ya tattarasu cikin a zaba mai radadi.
Allah ka nuna mana ranar da za a fatattaki zalunci a wannan kasa.

Allah zai cika hasken sa ko da kafurai da munafukai sunki.

KNPRSCD 07
Isiya-Sy ✍️
Kaduna Press

Post a Comment

0 Comments

Close Menu