Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Korea Ta Arewa Ta Bayyana Shugaban Kasar Amurka Da Rikitaccen Shu’umin Tsoho


Bayanin na kasar Korea Ta arewa ya zo ne a matsayin mayar da martani akan sakon Twitter da shugaba Donald Trump ya wallafa da a ciki ya bayyana cewa; Shugaban Korea ta arewan ne zai yi asara idan ya dauki matakan nuna adawa da amfani da karfi.

Babban jami’i mai shiga tsakanin tattaunawar da ake yi akan Nukiliyar kasar, Kim Jong Tshoul ya ce; Kasarsa ba za ta mika kai bori ya hau ba a matsin lambar da Amurka ta ke yi wa ma ta.

A ranar 12 ga watan Yuni 2018 ne aka yi ganawar farko a tsakanin shugabannin kasashen Amurka Donald Trump da na Korea Ta Arewa, Kim Jong Un a kasar Singapore.

Bangarorin biyu sun cimma matsaya akan kwance damarar makaman Nukiliya na kasar Korea.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu