Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Kotu A Saudiya Ta Yanke Hukumcin Kisa Kan Mutane 5 Da Laifin Kisan Khashoggi

Wata kotu a kasar Saudiya ta yanke hukumcin kisa kan wasu mutane guda 5 da aka kama da hannu wajen kashe fitaccen dan jaridar nan dan asalin kasar, Jamal Khashoggi, da ke zaune a kasar Amurka.

An kashe shi ne a karamin ofishin jakadancin Saudiya da ke kasar Turkiya, a watan Oktoban shekara ta 2018. Ya zuwa yanzu babu labia da gawarsa, da ake kyautata zaton an yi gunduwa gunduwa da ita ne.

Da dama daga cikin masharhanta suna nuna yatsa ga hukumar leken asirin Amurka CIA da kuma yarima mai jiran gado na kasar Saudiya Mohammad Bin Salman da bada Umarnin kashe shi, zargin da tuni yariman ya musanta. Har ila yau bayan wannan hukuncin da kotun ta yanke a asirce ta yanke wani hukunci kan wasu mutane 3 na tsawon shekaru 24 a gidan yari,kan batun da ya shafi dan rahoton gidan talbijin din Aljazeera.

A farko-farkon lamarin dai Saudiya ta bayyana cewa tana da labarin shigarsa ofishin jakadancinta a Turkiya amma daga bisani kuma ya fita, don haka ba’a kashe shi a ofishinta ba. Jamal ya shiga ofishin jakadancin ne a ranar biyu ga watan Oktoba domin sanya masa hannu kan wasu takardunsa da ya saki tsohuwar matarsa yadda zai iya sake yin wani auren. Ya zuwa yanzu dai gwamnatin Saudiya ta ki bada gawarsa kuma ta ki fadin inda ta ajiye.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu