Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta zama zakarun gasar zakarun nahiyar turai ta zamo zakara agasar cin kofin zakarun nahiyoyi da aka kammala.

Kungiyar kwallon kafan ta Liverpool ta zamo zakara ne bayan ta doke kungiyar kwallon kafa ta Flamengo na kasar Brazil daci 1 da nema bayan ankai ruwa rana adaidai mintina na 99 ta hannun dan wasa Roberto Fermino.

Bayan wannan nasarar kungiyar Liverpool ta zama kungiya ta biyu a Ingila da ta taba lashe kofin gasar, bayan Manchester United da ta dauki kofin a 2008

A karshen gasar dai kungiyar Liverpool ita ce ta daya sai kuma Flamingo da ta zo na biyu sai kuma kungiyar Monterrey ta Mexico ta zo ta uku bayan ta doke Al Hilal ta Saudiyya 4-3 a bugun fanariti bayan sun tashi kunnen doki da ci 2-2.