Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Kungiyar Taliban Ta Kai Hari Kan Tawagar Sojojin Amurka Ta Halaka soja 1 A Afghanistan.


Rahotanni da muka samu daga kasar Afghanistan sun bayyana cewa Kakakin kungiyar Taliban Zabuhullah Mujahid ya shaidawa manema labarai cewa mayakansu sun tarwatsa wata motar sojojin Amurka a garin Char Dar a lardin Kunduz da ke Arewacin kasar, da hakan ya jawo kashe sojan Amurka guda tare da jikkata wasu ciki har da sojojin kasar Afghanistan, mako guda bayan da bangarorin biyu suka fara tattaunawa sulhu a tsakaninsu.

Ana ganin wannan harin zai shafi tattaunawa sulhu da aka fara tsakanin kungiyar ta Taliban da kuma Amurka a birnin Doha na kasar Qatar a farko –farkon watan Disamba. Sai dai an samu tsaiko kadan bayan da mayakan Tailban din su ka kai hari kan sansanin sojin sama na Amurka dake Kabul.

Daga karshe bangarorin biyu sun cimma matsaya inda Amurka za ta janye dubban sojojinta da ke Afghanistan yayin da ita kuma kungiyar Taliban za ta bada lamunin tabbatar da tsaro. Wannan hari ya zo ne kwana daya bayan sanar da sakamakon zaben shugaban kasar, da ke nuna cewa shugaba mai ci a yanzu Asharaf Ghani ya kama hanyar lashewa a wani wa’adin mulki na biyu. Sai dai mayakan Taliban na daukarsa a matsayin dan koran Amurka.

Wannan ya sa su ka ki tattaunawa da gwamnatinsa.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu